OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan Daba Sun Kashe Mutum 2, sun Raunata Wasu a Bauchi

'Yan Daba Sun Kashe Mutum 2, sun Raunata Wasu a Bauchi

Photo Source: The Guardian

An samu tashin hankali lokacin da wasu ’yan daba suka kai hari a wani dakin pati inda suka kashe mutum biyu tare da raunata wasu a Bauchi.

‘Yan bindigar sun kai farmaki ne da bindigogin gargajiya suna harbe-harbe kai-tsaye a wurin da ke Gudun-Hausawa, wani karamin gari a birnin jihar.

Wasun su na dauke da adduna tare da yi wa da yawa daga ciki rauni.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi SP Ahmed Muhammed Wakil ne ya tabbatar da hakan.

Ya bayyana cewa rundunar ta kama mutane bakwai masu alaka da wannan aika aika-aikan.

Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi Umar Sanda ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Da yake zantawa da wakilin jaridar Leadership kamar yadda AllNews Nigeria ta tattaro, SP Wakil ya bayyana cewa, “Akwai wani lamari da wasu ‘yan daba suka shiga wani gida suka fara dukan jama’a da matasa, sai suka fara amfani da bindigar gargajiya wajen harbin mutanen da sassara su tare da raunata wasu matasa."

‘Yan ta’addan sun harbe matasa biyu tare da kashe su, Christopher Habila dan shekara 17 da Halon Nandir mai shekaru 18 dukkan su a Gudum Hausawa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci