OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

‘Yan bindiga sun sace tsohon kwamishina da kashe mutum biyu a Adamawa

‘Yan bindiga sun sace tsohon kwamishina da kashe mutum biy

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da tsohon kwamishinan gidaje da tsara birane, Injiniya Babangida Abubakar Idris a jihar Adamawa.

An harbe wasu mutum biyu har lahira yayin harin da aka kai gidan tsohon kwamishinan a ranar Talata.

Masu garkuwa da mutanen sun kewaye gidan da ke unguwar Bajabure a karamar hukumar Girei ta jihar.

AllNews ta tattaro cewa an harbi tsohon kwamishinan ne a kafa kafin a tafi da shi yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

A halin da ake ciki wata majiya na kusa da iyalen sa ta bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 30 a ranar Laraba.

Wata majiya da ba a bayyana sunanta ba ta ce tsohon kwamishinan ya tsallake rijiya da baya a wani hari da aka kai masa a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a jihar.

Majiyar ta ce, “Abin tashin hankali shi ne, a lokacin zaben fidda gwani na APC da ta gabata, ya tsallake rijiya da baya, inda wasu mutane suka kai masa farmaki inda suka farfasa gilashin motarsa."

Kakakin rundunar ‘yan sanda a Yola, SP Suleiman Nguroje ya ce rundunar ta samu rahoton yayin da take tabbatar da faruwar lamarin.

Nguroje ya ce tuni rundunar ta fara aikin ceto.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci