OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan Bindiga Sun Sace Babban Likitan Asibiti A Zamfara

'Yan Bindiga Sun Sace Babban Likitan Asibiti A Zamfara

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da babban Daraktan asibitin Dansadau da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.

An sace daraktan mai suna Dr Mansur Muhammad ne a Mashayar Zaki kan hanyar Gusau zuwa Dansadau.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban kungiyar likitocin Najeriya reshen Zamfara, Dokta Mannir Bature ya ce kungiyar ta samu rahoton cikin mamaki. 

Ya ce, “Muna kira ga mambobin mu da sauran jama’a da su sanya shi da sauran wadanda ake tsare da su a cikin addu’o’in su, yayin da kungiyar ke aiki da hukumomin da abin ya shafa don ganin an sako shi cikin koshin lafiya."

Ku tuna cewa jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin arewa maso yamma da ke fama da matsalar 'yan bindiga. 

Hanyar Gusau zuwa Dansadau na daya daga cikin hanyoyin da matafiya ke korafi kan ayyukan ‘yan bindiga.

Rahotanni sun bayyana cewa, an yi garkuwa da mutane da dama a kan hanyan a baya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai