OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Wata da ya shude

‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an JTF Biyu, Sun Tafi Da Dimbin Mutane A Kaduna

‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an JTF Biyu, Sun Tafi Da Dim

Bayan wani harin da aka kai a unguwar Sabon Gero da ke Millennium city na karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna, wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’an JTF biyu.

‘Yan bindigan sun kuma yi awon gaba da mutane da dama da suka hada da wani masanin magunguna da matar sa.

Sai dai a cewar rahotanni, shida daga cikin mutanen da aka sace sun tsere daga hannun 'yan bindigan. 

A cewar majiyoyi, an kai harin ne a ranar Laraba da misalin karfe 1 na safe.

Wata majiya ta bayyana cewa ‘yan bindigan sun shigo garin ne yayin da wasu suke aikace-aikace. 

Majiyar da ta so a sakaya sunanta ta ce, “’yan bindigan sun shiga gidajen mutane sun tafi da su, sun kuma kwashe wasu mazauna garin a lokacin da suke kokarin guduwa,” kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A halin da ake ciki mutanen biyu na JTF sun rasa rayukan su ne a kokarin dakile harin.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bakin mai magana da yawun ta, DSP Mohammed Jalige bata fitar da wata sanarwa ba. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai