OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

'Yan Bindiga Sun Bude Wuta Kan Sarakunan Gargajiya A Imo

'Yan Bindiga Sun Bude Wuta Kan Sarakunan Gargajiya A Imo

Hoto Daga: PremiumTimes

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun bude wuta kan sarakunan gargajiya a jihar Imo inda mutum uku suka mutu.

'Yan bindigan sun kai harin ne a garin Nnenasa, Hedikwatar karamar hukumar Njaba dake jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa, sarakunan gargajiya daga yankin da yawansu ya kai kimanin 20 suna cikin taro yayin da ‘yan bindigar suka mamaye wurin taron.

Haka kuma suka katse taron da harbe -harbe inda suka kashe a kalla sarakunan gargajiya uku nan take.

An garzaya da wadanda suka samu raunuka na harbin bindigan zuwa asibiti da ke kusa da su domin kula da lafiyarsu.

Da yake tabbatar da faruwan lamarin ga jaridar AllNews, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Imo, Mike Abatam, ya ce "sarakunan gargajiya uku ne kacal aka tabbatar sun mutu".

Abatam ya kara da cewa a halin yanzu ana ci gaba da bincike kuma nan ba da dadewa ba za'a samu karin Bayani.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci