OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yajin Aiki: Kungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya Ta Sake Tsunduma Yajin Aiki

Yajin Aiki: Kungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya Ta Sake Ts

Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta kara tsawaita yajin aikin da take yi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa an cimma wannan matsaya ne bayan taron majalisar zartarwar kungiyar ta kasa da ya gudana a hedikwatar kungiyar da ke Jami’ar Abuja a safiyar ranar Litinin.

Duk da dai cikakkun bayanai ba su bayyana ba har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto, sai dai an san cewa ba a samu matsaya tsakanin kungiyar malaman da kuma gwamnatin tarayya ba kan bukatun da suke neman a biya musu.

Kwanan nan aka ji Shugaban na ASUU Emmanuel Osodeke ya shawarci Shugaba Muhammadu Buhari da ya yi koyi da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ta hanyar da ya bi don warware matsalolin tare da kawo karshen yajin aikin da aka fara a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022.

Bugu da kari A baya anji Osodeke ya yi wa wasu jami’o’i kaca-kaca sakamakon yanke shawarar janye yajin aiki, inda ya ce ba su da wani amfani.

Sai dai ya fito ya bayyana cewa shi fa ba haka yake nufi ba 'yan jarida ne basu fahimce shi ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai