OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 4 Kwanaki da suka gabata

Yadda Shugaban Karamar Hukuma Ya Yanke Jiki Ya Mutu A Nasarawa

Yadda Shugaban Karamar Hukuma Ya Yanke Jiki Ya Mutu A Nasara

Nasarawa state

Shugaban karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa, Emmanuel Leweh ya mutu.

Shugaban ya mutu ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja ranar Alhamis.

Marigayin wanda ya shafe watanni uku yana mulki ya yanke jiki ya fadi bayan wata taron majalisar sa a ranar Litinin din da ta gabata.

An gabatar da taron ne a sakatariyar karamar hukumar ta Akwanga.

Mista Samuel Tsebe, dan majalisar dokokin jihar Nasarawa ne ya tabbatar da labarin mutuwar.

Yayin da yake mika sakon ta’aziyyar sa, Tsebe ya ce, “Na rasa babban wa' na, Honarabul Joseph Leweh, shugaban zartarwa na karamar hukumar Akwanga a yammacin yau bayan gajeriyar rashin lafiya.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci