OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Yadda Manoman Dankali 600 a Gombe Suka Samu Tallafin Gwamnatin Tarayya

Yadda Manoman Dankali 600 a Gombe Suka Samu Tallafin Gwamnat

Hoto Daga: Vanguard

Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara (FMARD) ta baiwa manoman dankali 600 ikon bunkasa noman abinci a jihar Gombe.

Ma’aikatar ta raba irin dankalin turawa kusan dubu goma sha biyu kyauta ga manoman.

Alhaji Muhammad Sabo Nanono, Ministan Noma da Raya Karkara ya bayyana hakan lokacin da yake gabatar da ingantaccen irin dankalin turawan ga wadanda suka amfana a jihar ta Gombe.

Ministan ya ce ya zama wajibi ga gwamnati ta binciko wasu hanyoyin ciyar da kasar nan tare da samun kudaden waje ta hanyar tallafin Noma.

Kodinetan jihar Gombe na FMARD, Dakta Musa Muhammad Inuwa wanda ya wakilci Ministan ya ce kowanne daga cikin  wadanda suka ci gajiyar tallafin, zai mallaki irin dankalin turawan dari biyu, kuma ya bukace su da su yi amfani da su yadda ya kamata.

Kwamishinan aikin gona da kiwon dabbobi na jihar Gombe, Muhammad Magaji Gettado ya bayyana cewa rarraba kayayyakin zai bunkasa noman abinci tare da magance talauci a tsakanin manoman jihar.

Yayin da yake yabawa Gwamnatin Tarayya saboda wannan karamcin, ya roki Gwamnatin Tarayya da ta taimaka wa manoma da injunan sarrafawa domin kara darajar kayayyaki da samun abin ci daga gare ta.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai