OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Wata Kungiya ta bukaci a tsige Yahaya Bello daga matsayin kodinetan matasa na yakin neman zaben Tinubu

Wata Kungiya ta bukaci a tsige Yahaya Bello daga matsayin ko

Wata kungiya a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi kira da a tsige gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a matsayin kodinetan majalisar matasa a yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar.

Kungiyar ta masu goyon bayan Shugaban kasa (PSC), ta ce ya kamata a cire Mista Bello daga mukamin da aka basa sannan a sauya kujerar zuwa kudu.

A makon da ta gabata ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya bayyana sunan gwamnan jihar Kogi a matsayin kodinetan wayar da kan matasa na majalisar yakin neman zaben sa.

Kassim Muhammad, shugaban kungiyar, a wata sanarwa da ya bayyanawa manema labarai a ranar Litinin, ya ce kasancewar Mista Bello yana adawa da kudurin karba-karba hakan yasa wannan matsayi bai dace dashi ba.

Kassim ya kara da cewa yahaya Bello ba ya cikin jerin matasa, a nemi wani mukami daban a bashi amma ba kodinetan matasa ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci