OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Watanni da suka shude

Wata bakuwar cutar ta karshe mutum 11 a Gombe

Wata bakuwar cutar ta karshe mutum 11 a Gombe

79,329 Vulnerable Groups May Be Denied Access To Healthcare In Kaduna – Official

Wata baƙuwar cuta ta ɓulla a ƙauyen Chessi da ke gundumar Kulani a yankin ƙaramar hukumar Balanga, inda ta kashe mutum 11 tare da kwantar wasu 30 a asibiti.

Tawagar likitocin da suka ziyarci yankin sun fayyace cewa cutar ba kwalara ba ce amma sun ɗauki samfurin jini da ruwa na waɗanda suka kamu da cutar don gudanar da gwaji.

Sun bayyana cewar mutum 30 na kwance a asibiti, inda cutar ke da alamun ciwon kai, zazzabi, ciwon ido da kuma ciwon ciki.

Likitocin sun shawarci al’umma da su kai rahoton duk wasu da ake zargi da kamuwa da cutar ga cibiyar lafiya da aka kafa a makarantar firamare ta garin Chesi.

Ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Balanga ta Arewa, a majalisar dokokin jihar, Musa Buba, ya bayar da tallafin magunguna da kayayyakin masarufi na sama da miliyan 1.5 ga al’ummar yankin Chessi.

 

 

Buba, ya ce ya bayar da wannan tallafi ne a lokacin da ya ji rahoton ɓullar cutar, ya kuma ya gode wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa aikewa da tawaga daga ma’aikatar lafiya da kuma cibiyar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta ƙasa (NCDC).

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci