OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Wata da ya shude

Tinubu Ya Bar Najeriya Zuwa Kasar Faransa

Tinubu Ya Bar Najeriya Zuwa Kasar Faransa

Zababben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bar Najeriya zuwa kasar Faransa.

Dan takarar shugaban kasan kuma jigon jam’iyyar APC ya tashi ne jim kadan bayan ganawar sa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da safiyar yau Litinin.

Kakakin sa Tunde Rahman ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

A halin da ake ciki kuma Rahman bai bayyana lokacin da dan takarar shugaban kasan na APC zai dawo ba.

Sai dai ya bayyana cewa Tinubu zai dawo nan ba da jimawa ba.

Sanarwar ta kara da cewa, "Ya tafi birnin Paris na kasar Faransa domin gudanar da wasu muhimman taro."

Ku tuna cewa Tinubu ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC don wakiltar jam'iyyar a zaben 2023 a ranar 8 ga watan Yuni na 2022.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai