OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Takaitattun Muhimman Labarun Karshen Mako Na 15 Ga Watan Oktoba 2021

Takaitattun Muhimman Labarun Karshen Mako Na 15 Ga Watan Okt

Hoto Daga: PremiumTimes

RUNDUNAR SOJIN NAJERIYA TA TABBATAR DA MUTUWA SHUGABAN ISWAP ABU MUSA AL-BARNAWI

Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar Shugaban ISWAP Abu Musab Al-Barnawi.

Rundunar ta tabbatar da Hakan ne a ranar alhamis a fadar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja.

A cewar Hafsan Hafsoshin Tsaro, Janar Lucky Irabor, "Ya mutu kuma zai ci gaba da kasancewa matacce."

Sai dai Kuma baya ga haka janar din bai bada Karin bayani ba.

A watan satumban da ta gabata ne rahotanni suka nuna cewa an kashe Shugaban ISWAP din Amma har yanzu Kungiyar batace komai ba.

Haka Kuma Rundunar Sojin Najeriyan ta nisantar da kanta daga Sheikh Ahmad Gumi, wani malamin addinin Islama wanda ke jagoranci tattaunawa da 'yan fashi.

Rundunar tace aikin kai yakeyi ba na rundunar ba.

 

MAJALISAR JIHAR ZAMFARA TA DAKATAR DA MAMBOBINTA BIYU KAN ALAKA DA 'YAN BINDIGA

 

A ranar talatan da ta gabata ne Majalisar jihar Zamfara ta dakatar da mambobinta guda biyu kan zargin alaka da yan bindiga.

A cewar jami'in hulda da jama'a na majalisar, Mustapha Jafaru Kaura, an dakatar da ƴan majalisar ne na tsawon wata uku kafin a kammala bincike kan zargin.

Jafaru ya Kara da cewa kwamitin da'a da tsaro na Majalisar ne zasu binciki wadanda Ake zargin.

Yan majalisar da aka dakatar sun hada da Yusuf Muhammad Anka da ke wakiltar karamar hukumar Anka da kuma Tukur Bakura dan majalisa da ke wakiltar Bakura.

A lokacin da Majalisar ta yanke hukuncin, Yan Majalisar da Ake zargin basu halarci zaman ba.

 

SOJOJIN NAJERIYA SUN KASHE 'YAN FASHIN DAJI FIYE DA 40

Sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe 'yan fashin daji fiye da 40 a arewa mason yemma. 

A cewar rundunar Sojin, nasarar ta samu ne cikin makonni biyu a jihohin Sokoto da Kaduna.

Muƙaddashin shugaban sashen yaɗa labarai na rundunar, Benard Onyeuko ne ya sanar da faruwan lamarin ranar alhamis a Abuja.

Ya Kara da cewa hare-haren da aka gudanar sun bada nasarar lalata sansanonin 'yan bindigar da dama.

Zaku Iya tunawa cewa babban Hafsan Sojin najeriya, Janar Farouk Yahaya ya gaddamar da wasu ayyukan Soja guda uku don dakile matsalar tsaro a kasar.

Ayyukan da ya kaddamar a farkon watan oktoban nan sun hada da Golden Dawn da Still Water da kuma Enduring Peace.

 

ZULUM YA TARBI 'YANMATA SHIDA DA SUKA TSERE HANNUN BOKO HARAM

Daga arewa maso gabashin najeriya Kuma, Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya tarbi 'yan mata shida da suka tsere daga hannun Boko Haram.

Kwamishinan harkokin mata, Hajiya Zuwaira Gambo ce ta gabatar da ‘yan matan da suka tsere masu shekaru tsakanin 20 zuwa 25.

A cewar ta, 'yan matan sun tsere daga hannun‘ yan ta’addan ne a Buni Yadi dake jihar Yobe, sannan suka yi tafiyan awanni 6 ta dajin Sambisa kafin jami’an tsaro su kubutar da su.

Zaku tuna cewa, a ranar 14 ga watan Afrilun 2014 ne 'yan ta'addan Boko Haram suka mamaye makarantar sakandaren' yan mata ta Chibok inda suka sace dalibai mata sama da 200, kuma tun daga lokacin sama da 100 daga cikinsu suka tsere yayin da aka sako wasu bayan tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan ta'addan.

Zulum ya karɓi waɗanda suka tseren da 'ya'yan su cikin farin ciki a ofishinsa da ke Sakatariyan Musa Usman dake Maiduguri.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati na yin duk kokarin ta na tabbatar da sake ginawa da kuma dawo da duk wadanda harin ta’addancin Boko Haram ya rutsa da su.

 

EL-RUFA'I YA SHA ALWASHIN RUFE WASU MAKARANTU A KADUNA

A wata rahoton Kuma, Gwamnatin jihar Kaduna ta sha alwashin rufe dukkan makarantun horar da maikatan jinya masu zaman kansu wanda ba su da rajista a jihar.

Gomnatin tace Hakan ya zama dole don kare Mutane daga gurbatattun ma’aikatan lafiya.

A cewar Kwamishinan lafiya ta jihar Kaduna, Dakta Amina Mohammed Baloni, makarantun suna aiki ba bisa ka’ida ba.

Ta kara da cewa makarantun kuma ba su da kayan aiki, karfin ma’aikata da izini daga kungiyoyin kwararru da ake bukata.

Kwamishinan wacce ta yi magana a wani taron tattaunawa na kwana ɗaya kan harkan lafiya, ta bayyana shirin gwamnati na inganta fannin kiwon lafiya ta hanyar samar da motocin daukar marasa lafiya a cibiyoyin Kiwon lafiya na matakin farko a duk fadin jihar.

Zaku samu labarai da wasu shirye-shiryen mu a harshen Turanci kan adireshin mu na yanar gizo wato www.allnews.ng

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci