OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Sokoto: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Tsare Wani Darakta Bisa Badakalar Aiki

Sokoto: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Tsare Wani Darakta Bisa  Ba

Wata babbar kotun tarayya da ke Sokoto a ranar Larabar da ta gabata ta bayar da umarnin a tsare wani darakta a hukumar kula da kayayyaki ta jihar Sokoto, Hassan Bello, a gidan gyaran hali bisa zargin badakalar naira miliyan 1.3 na aiki.

Mai shari’a Ahmad Mahmud shi ne, ya bayar da umarnin a tsare Hassan Bello bisa kamasa da laifi.

Mista Mahmud ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 4 ga watan Oktoba, domin cigaba da sauraren karar neman belin da kuma shari'a.

Hannafi Sa'ad ma'aikaci a Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ya shaida wa kotu cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne tun a watan Agustan shekarar 2021.

Ana zargin Bello, wanda shi ne Daraktan gudanarwa na hukumar da karbar kudaden ne daga hannun Aliyu Adamu-Tsaki, Yusuf Abubakar da Yahaya Salihu a gaban Dahiru Muhammad a Sokoto.

EFCC ta yi zargin cewa wanda ake tuhumar ya gabatar musu da takardun aiki na karya wanda daga baya aka gano na karya ne kuma babu su.

 

 

NAN

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai