OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Wata da ya shude

Sojoji Sun Kashe 'Yan Ta'adda 82 A Zamfara

Sojoji Sun Kashe 'Yan Ta'adda 82 A Zamfara

Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar kawar da 'yan ta'adda 82 a jihar Zamfara.

Rundunar ta yi wa ‘yan ta’addan ruwan bama-bamai ne ta sama a lokacin da suka zo yin barna a Rafin Dankura da ke karamar hukumar Bakura a jihar.

An bayyana hakan ne a wata zantawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Abuja ranar Alhamis ta hannun Daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Maj.-Gen. Benard Onyeuko.

Onyeuko ya bayyana cewa dakarun Operation Hadarin Daji sun amsa kiran gaggawa cewa ‘yan ta’addan na kokarin sace mutane wanda ya kai ga kashe 82 daga cikinsu.

Ya kara da cewa ‘yan ta’addan da suka hada kansu sama da 150 sun shirya kai hari kauyen Kofar Danya karamar hukumar Bukkuyum dake jihar.

Ya kara da cewa rundunar sojin saman Najeriya ta fatattaki ‘yan ta’addan ta hanyar kai hare-hare ta sama wanda ya halaka da yawa daga cikinsu.

Kayayyakin da aka kwato a yayin farmakin sun hada da bindigogi kirar AK 47 guda biyu, gurneti kirar 36 guda, ​​wayoyin hannu guda biyu da kuma kudi N211,915 yayin da aka ceto wasu fararen hula shida da aka yi garkuwa da su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai