OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Wata da ya shude

Shugaba Tinubu zai yiwa al'umma jawabi

Shugaba Tinubu zai yiwa al'umma jawabi

Shugaba Bola Tinubu zai yi wa al’ummar kasar nan jawabi a kafafen yada labarai a ranar Lahadi, 4 ga watan Agusta, 2024, da misalin 7 na safe.

 

Wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Cif Ajuri Ngelale, ya sanya wa hannu a yammacin ranar Asabar.

 

Ya ce an umarci gudajen talabijin, rediyo, da sauran kafafen yada labarai da su watsa shirin ka-tsaye.

 

“Za a sake maimaita shirin a NTA da FRCN da misalin karfe 3 na yamma da 7:00 na daren wannan rana,” in ji Ngelale.

 

Wannan dai ba zai rasa nasaba da zanga-zangar da ake gudanar a fadin Nijeriya a wasu yankunan kasar dai al’amura sun tabarbare, inda lamarin ya zama tashe-tashen hankula. ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci