OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Shugaba Buhari Zai Tafi Taron Karfafa Dangantaka Tsakanin Turkiyya Da Afrika

Shugaba Buhari Zai Tafi Taron Karfafa Dangantaka Tsakanin Tu

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai bar gida Najeriya zuwa babban birnin Istanbul Turkiyya domin halartar taron karfafa dangantaka tsakanin Turkiyya da Afrika karo na uku wanda Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya shirya.

 Mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau Alhamis.

Sanarwar ta ce taron zai mayar da hankali ne wajen kara hadin kai tsakanin kasashen Afrika da Turkiyya.

Cikin wadanda za su raka shugaban zuwa Turkiyya har da uwargidansa Aisha Buhari da kuma ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama da ministan tsaro Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya.

Haka kuma akwai ministan Abuja Mohammed Bello da ministan lafiya Osagie Ehanire da ministan noma Mohammed Abubakar da ministan masana'antu da cinikayya Adeniyi Adebayo da kuma babban mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno.

Tafiyar Shugaba Buhari dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ‘yan kasa ke cikin wani yanayi na rashin tsaron da yaki ci ya ki cinyewa.

A cikin mako guda kawai, yan bindiga sun kai hari kan matafiya a hanyar Kaduna zuwa Zaria, da hanyar kaduna zuwa Abuja, da wasu a Zamfara da wasu makamantan su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci