OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Shugaba Buhari Ya Jagoranci Tunawa Da Mazan Jiya

Shugaba Buhari Ya Jagoranci Tunawa Da Mazan Jiya

Shugaba Buhari Da Farfesa Osinbajo

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo, da ‘yan majalisar tarayya, da jami’an diflomasiyya domin karrama sojojin da suka rasa ran su a bakin aiki a yau Asabar.

Taron wanda ya hada da shimfida furanni a babban filin ajiye motoci na kasa da ke Abuja, shi ne kololuwar manyan ayyukan da aka shirya domin bikin tuna zagayowar ranar tunawa da sojojin (AFRDC).

shugaban kasar ne wanda ya fara shimfida furannin, sai mataimakin sa, shugaban majalisar dattawa, sai kuma kakakin majalisar wakilai, da alkalin alkalan Najeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari

Shi ma Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya, da takwaran sa na babban birnin tarayya, Malam Mohammed Bello sun  shimfida furannin.

Babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor; Hafsan Sojoji, Laftanar-Janar. Faruk Yahaya; Shugaban hafsan sojin sama Air Marshal Isiaka Amao da babban hafsan sojin ruwa Vice Admiral Awwal Gambo ne suka yi atisaye yayin bikin.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya ruwaito cewa akan yi wannan biki ne a duk fadin duniya don tunawa da sadaukarwar da ‘yan kasar suka yi domin samar da zaman lafiya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai