Emir Aminu Ado Bayero
Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya nuna alhininsa ga wadanda suka gamu da ibtila'i a lokacin gudanar da zanga-zanga a ranar alhamis din da ta gabata a jihar Kano.
Wannan na kunshe cikin wata Sanarwa da Sakataren Sarkin Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa premier Radio jiya Jumaa.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce duk lokacin da aka shiga matsi na rayuwa ana son bawa ya zama mai kusantuwa ga Allah ya Kai kukansa domin shi ne zai share Masa hawaye.
Sarkin yayi kira ga Al'ummar Kano su zauna lafiya sannan su guji tashin hankali da taba dukiyoyin gwamnati da na sauran Al'umma.
Tuni dai Mai Martaba Sarkin ya fara shirye shirye domin jagorantar tawagar wakilai daga jihar Kano inda zasu tafi domin isarwa da Shugaban kasa koken Al'ummar jihar Kano da suka bashi a lokacin da sukayo tattaki zuwa fadarsa.
A saboda Haka ne Mai Martaba Sarkin Alhaji Aminu Ado Bayero ya sake jaddada bukatar Al'umma su cigaba da addu'a, sannan iyaye su kula da tarbiyyar yayansu inda yace Manzon Allah S.A.W yace kowannen ku makiyayi ne kuma za a tambaye shi a kan abin da aka bashi kiwo ranar gobe kiyama.
Daga nan yayi adduar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu ya kuma bawa wadanda suka samu raunuka lafiya tareda mayarwa wadanda suka rasa dukiyoyinsu fiye da abunda suka rasa.
0 Tsokaci