OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Sallah: El Rufa'i ya yi kira da a yi addu'o'i, a bi ka'idoji na Covid-19

Sallah: El Rufa'i ya yi kira da a yi addu'o'i, a bi ka'idoji

Gomna Nasir El-Rufai| Hoto Daga: BBC

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya yi kira da a yi wa jihar da Najeriya addu'oi a cikin wadannan mawuyacin lokaci.

Gomnan ya kuma yi kira da a bi ka'idoji na Covid19 yayin da musulmai ke bikin babban sallah.

A cikin sakon taya murna wanda mai ba wa gomnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa, Mista Muyiwa Adekeye ya sa hannu, gwamnan ya bukaci Musulmai da su yi koyi da misalin imani da sadaukarwa da Sallah ke nunawa.

Gwamnan ya kuma yaba da juriyar 'yan kasa a wannan mawuyacin lokaci sannan ya yi addu'ar neman albarkar Allah game da hakurin da ake yi.

 El-Rufai ya bukaci al'ummar musulmai da kar su cire rai, kuma su yi bikin sallar bisa kiyaye ka'idojin kiwon lafiyar jama'a.

Yace hakan an tsara ne don kare kowa daga sabuwar launin cutar Covid19 wato Delta, wacce take saurin yaduwa kuma tuni ta ke yaduwa a wasu jihohin kasar.

Gwamnan ya yi kira ga dukkan al’ummomin da ke jihar ta Kaduna da su tabbatar da zaman lafiya da juna, duk da kalubalen tsaro da ke addabar al’ummomin da dama.

Sanarwar ta kuma bukaci dukkan mazauna yankin da su kasance masu lura da bin doka yayin da hukumomin tsaro ke kara kokari wurin yaki da 'yan ta'adda don kare al'ummomi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci