OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Wata da ya shude

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Tabbatar Da Rahoto Sace Basaraken Gargajiya A Ebonyi

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Tabbatar Da Rahoto Sace Basaraken G

Nigerian Police

Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi ta tabbatar da rahoton yin garkuwa da basaraken yankin Isu da ke karamar hukumar Onicha ta jihar, Cif Ambrose Ogbu.

‘Yan bindigan sun yi garkuwa da Ogbu a fadar sa ranar Alhamis.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, Kakakin Rundunar, SP Chris Anyanwu, ya ce ‘yan sanda sun san da faruwar lamarin.

Ya ce, “Eh, muna sane da labarin sace basaraken. Ya faru ne a Isu, Onicha."

Ya kara da cewa har yanzu ba a bayar da cikakken bayani kan lamarin ba.

Wata majiya da ke kusa da iyalan sarkin ta bayyana cewa an yi garkuwa da basaraken ne tsakanin karfe 8 zuwa karfe 9 na daren Laraba.

Majiyar ta ce, “An yi garkuwa da shi ne a fadarsa.

“Masu garkuwa da mutane sun zo da babura da yawansu, suka umarci mai gadi da ya kira basaraken.

"A yayin da basaraken ke fitowa, masu garkuwa da mutane sun tattara makullin motarsa ​​kirar Hundai SUV, inda nan take suka tilasta masa shiga motar suka tafi."

Majiyar da ta yi addu’ar Allah ya dawo da sarkin lafiya ta ce har yanzu masu garkuwa da mutanen ba su tuntubi dangin ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai