OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ranar 'Yancin Kai: Jonathan Ya Bukaci Yan Nijeriya Su Zama Masu Kishin Kasa Da Hadin Kai

Ranar 'Yancin Kai: Jonathan Ya Bukaci Yan Nijeriya Su Zama M

Yayin da Najeriya ke murnar samun ‘yancin kai, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bukaci ‘yan kasa da su kasance masu kishin kasa da kuma baiwa hadin kai muhimmanci.

 Goodluck Jonathan yayi wannan kiran ne ta cikin sakon fatan alherin daya gabatar a Abuja domin murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai.

Jonathan ya bayyana cewa lokacin zabe lokaci ne da ‘yan Najeriya za su nuna kishin kasa.

A cewar sa “yan uwa ’yan Najeriya, bikin mu na bana ya zo ne a daidai lokacin da al’ummarmu ke shirin gudanar da babban zabe Wanda lokaci ne mai mahimmanci a gare mu duka, domin  zaɓen ya ba da wata dama ga ƴan ƙasar mu nuna imaninmu ga ɗaukakar al'ummarmu"

"Mu kasance masu kishin kasa a zaben dake karatowa ta hanyar tantance Yan takarar da zasu ci da kasar gaba'

 ’Tsohon shugaban kasan ya kara da cewar "yan ƙasarmu sun mutane masu fikira, jajircewa, da daraja a fannoni daban-daban. Saboda Hakan akwai bukatar mu tsaya tsayin daka kan kishin kasa a lokacin da kasar nan ke fuskantar kalubale da dama.

Mu zama masu nuna juriya a lokutan da muka cikin matsin rayuwar, mun kuma yi iya bakin kokarin tabbatar da zaman a duk lokacin da bata gari suka yi yunkurin kawo was zaman lafiyar mu barazana" in ji shi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai