OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

PDP Ta Shirya Karbar Goje Yayin Da Ya Fice Daga APC Ranar Laraba

PDP Ta Shirya Karbar Goje Yayin Da Ya Fice Daga APC Ranar La

L-R Senator Mohammed Danjuma Goje, Governor Muhammadu Inuwa Yahaya| Photo Source: Ripples Nigeria

Jam’iyyar PDP ta kammala shirye-shiryen karbar wani jigo a jam’iyyar APC a Gombe, Sanata Mohammed Danjuma Goje.

Goje wanda ya sauya ra'ayin sa a minti na karshe an ruwaito cewa zai fice daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa PDP ranar Laraba.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa wani mataimaki na kusa da Goje ya zanta da wakilinta inda ya tabbatar da faruwar lamarin.

Mataimakin wanda ya nemi a sakaya sunan sa ya ce an kammala duk wani shiri na sauya shekar Gojen zuwa PDP.

Ya bayyana cewa, "Ni ba mai magana da yawunsa ba ne amma na san cewa akwai irin wannan shirin."

Idan dai za a iya tunawa dai AllNews ta ruwaito cewa an dade ana takaddama tsakanin Sanatan da gwamnan jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya.

Rahotan sauya shekar Goje na zuwa ne bayan duk kokarin da ake na sasanta mutanen biyu bai cimma ruwa ba.

Mazauna garin sun ce an dade ana sa ran sauya shekar nasa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci