OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

PDP Ta Dage Ranakun Gudanar Da Zabukan Fid Da Gwani

PDP Ta Dage Ranakun Gudanar Da Zabukan Fid Da Gwani

Kwamatin Gudanarwa na jam'iyyar PDP ta sanar da dage lokutan gudanar da wasu zabukan fid da gwani na jam'iyyar kafin babban zaben badi.

A wata sanarwa da Sakataren Yada Labaran jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba ya fitar yau Alhamis, kwamitin ya bayyana cewa za a gudanar da zabukan kujerar gwamna ranar Litinin, 23 ga watan Mayun 2022, yayin da za a yi na sanatoci ranar Asabar, 21 ga Mayun.

Zabukan 'yan majalisar wakilai za su gudana ranar Juma'a, 20 ga Mayu, sai kuma na 'yan majalisar jiha da za a yi Laraba, 18 ga watan na Mayu.

Jami’iyyar ta kuma ce ta dage taron zabar wakilai wato daliget a dukkan kananan hukumomi na kasa, sai dai bata bayyana ranakun da zata gudanar da zabukan ba nan gaba,

Sanarwar ta tabbatar da cewa sauyin bai shafi zaben fid da dan takarar shugaban kasa ba, wanda tun farko aka tsara yin sa ranar 28 zuwa 29 ga Mayu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci