Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa (NANS), ta sanar da shirin fara zanga-zanga daga ranar 15 ga Satumba, kan ƙara farashin man fetur
A ranar Talata ne, aka samu ƙarin farashin man fetur daga Naira ₦568 zuwa ₦855 kan kowace lita a duk gidajen mai na Kamfanin NNPC.
Ƙarin farashin ya haifar da cece-kuce a faɗin ƙasar, inda ƙungiyoyin ma’aikata suka nemi a sauya sabon farashin nan take.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, shugaban Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa (NANS), Okunomo Henry Adewumi, ya buƙaci a gaggauta janye sabon farashin man fetur.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, za a gudanar da zanga-zangar ne cikin lumana kamar yadda doka ta tanada. “Mun rubuta ne domin sanar da ku game da wani gagarumin rufe dukkanim manyan biranen Najeriya, daga ranar 15 ga Satumba, 2024, domin nuna adawa da ƙarin farashin man fetur da aka yi".
“Muna kira ga ɗaukacin ɗaliban Najeriya da su farka da wannan kira na faɗakarwa, domin za mu mamaye manyan biranen ƙasar nan a ranar 15 ga Satumba, 2024.
“Ba za mu yi shiru ba, kuma ba za a tsorata mu ba. Za mu tashi tare domin neman ingantacciyar yarjejeniya ga ɗaliban Najeriya da talakawa."
“Muna roƙonku da ku ɗauki matakan da suka dace don tabbatar da doka da oda yayin rufe biranen, yayin da muke ba ku tabbacin cewa zanga-zangar tamu za ta kasance cikin lumana da doka,” in ji sanarwar.
0 Tsokaci