OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Na Ba Ku Sa'o'i 48 Ku Rufe Kamfanin Simintin Obajana: Gwamna Yahaya Bello

Na Ba Ku Sa'o'i 48 Ku Rufe Kamfanin Simintin Obajana: Gwamna

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayar da umarnin rufe kamfanin siminti na Obajana cikin sa'o'i 48.

 

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne majalisar dokokin jihar Kogi ta zartar da kudurin rufe kamfanin, biyo bayan gazawar Aliko Dangote nakin amsa gayyatar da akai masa.

 

Sannan, an sami rahoton cewa matasan jihar sun kutsa kai cikin kamfanin tare da far wa maaikatan.

 

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar Kingsley Fanwo, ya fitar a ranar Larabar da ta gabata, ya bayyana cewa gwamnati ta amince da yancin yan kasa su gudanar da zanga-zanga, amma kuma ya ce dole ne a mutunta kudurin majalisar dokokin jihar.

 

Gwamnan ya kuma bukaci mahukunta rukunin kamfanin Dangote da su tabbatar da cewa an rufe masanaantar siminti da ke Obajana cikin saoi 48 masu zuwa domin karrama umurnin da gwamnati ta bayar akan akan cewa a rufe masanaantar har sai kamfanin na Dangote ya baiwa majalisa takardun da ta bukata.

 

A matsayinmu na Gwamnati, za mu kare dukkan cibiyoyin gwamnati .

 

Gwamnan yana kuma tabbatar wa alummar jihar jajircewar sa wajen kare muradun su ba tare da wata matsala ba.

 

"A wannan gwagwarmayar jihar Kogi mai dauke da mutane sama da miliyan hudu za mu tabbatar da kare muradun jihar tare da kare mutuncin ta,da kuma alhaki tare da yin biyayya ta hanyar aiki da dimokuradiyya," in ji sanarwar.

 

Sai dai gwamnati ta bukaci jama'a da su ci gaba da zama 'yan kasa na gari, masu bin doka da oda da kuma bin tsarin mulki.

 

Rashin bin doka da oda ba za su amfanar da komai ba, domin muna fatan ci gaba da kasancewa yanki mafi zaman lafiya a Najeriya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci