OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Wata da ya shude

Mutum biyu sun gurfana gaban kotu bisa laifin sace kadarorin N968,000 a coci

Mutum biyu sun gurfana gaban kotu bisa laifin sace kadarorin

An gurfanar da wasu mutane biyu da ake tuhuma a gaban wata kotun majistare da ke birnin Ibadan bisa zarginsu da kutsawa cikin coci tare da yin awon gaba da kadarori na Naira 968,000.

Wadanda ake zargin da aka gurfanar a ranar Litinin din da ta gabata an bayyana sunayensu da Bidemi Emmanuel da Olatunji Johnson.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ta ruwaito, dan sanda mai shigar da kara, ASP Sikiru Ibrahim ya ce wadanda ake zargin sun kutsa cikin Cocin Lifeline Tabernacle da ke kan titin Ibadan Ring Road da misalin karfe 2 na safe a ranar 1 ga watan Yuni, inda suka yi awon gaba da kadarorin kusan Naira miliyan daya.

Kaddarorin sun hada da "fankoki 12 da kudinsu ya kai N516,000, LG TV mai inci 32 wanda kudin sa ya kai N35,000 da kyamarar bidiyo ta Canon guda daya da darajar ta ta kai N220,000."

Ibrahim ya kara da cewa mutanen biyu sun kutsa cikin cocin tare da wasu da ake nema ruwa a jallo. 

Ya bayyana cewa sauran kadarorin da aka sace sun hada da na’urar magana ta amsa kuwa da kudinsu ya kai N112,000, kwamfutar tafi-da-gidanka ta HP guda daya ta kai Naira 85,000 da kuma tsabar kudi N10,000.

Sai dai wadanda ake tuhumar sun ki amsa laifin da aka karanta a gabansu.

Yayin da ta dage sauraron karar zuwa ranar 11 ga watan Agusta, 2022, Alkalin kotun, Misis S.A. Adesina ta bayar da belin wadanda ake kara a kan kudi N200,000 kowanne da kuma mutum biyu masu tsaya masa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai