OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Wata da ya shude

Mutum 14 sun mutu a wani hatsarin mota a Jigawa

Mutum 14 sun mutu a wani hatsarin mota a Jigawa

Wani mummunan hadarin motoci daya afku a Babban titin kwanar Dumawa zuwa Babura ta jihar jigawa yayi sanadiyar mutuwar mutane 14.

 

Hadarin wanda ya faru tsakanin motar haice maidauke da fasinjoji goma sha hudu da wata babbar motar Daukar Kaya.

 

Wasu wanda hadarin ya faru agaban idonsu sun shaida cewar mutane goma sha hudu ne suka rasa ransu yayin hadarin yayi da mutum huɗu suka jikkata.

 

Rahotanni sun bayyana cewar galibin wanda hadarin ya rutsa da su yan kasuwa ne inda suka nupi zuwa garin kanya Babba domin cin kasuwar mako mako dake ci ranar Talata.

 

Kawo yanzu dai Hukumar kiyaye afkuwar hadura bata fitar da wani bayani a hukumance ba game da sanadiyar afkuwar hadari.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci