OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Muna Aiki Tukuru Don Sauke Farashin Kayan Abinci, Cewar Gwamnatin Tarayya

Muna Aiki Tukuru Don Sauke Farashin Kayan Abinci, Cewar Gwam

Shugaba Muhammadu Buhari

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana aiki tukuru ta hanyoyi da dama don durkusar da farashin abinci Najeriya.

 

Hakan ya zo ne cikin bayanin Ministan Noma da Raya Karkara, Mohammed Abubakar a Abuja.

 

Ministan ya yi bayanin ne yayin wata ziyarar rangadin sanin makamar aiki tare da hukumar binciken noma ta Najeriya.

 

Abubakar ya kara da cewa sha’awar noma sosai ce ta sa shugaba Muhammadu Buhari ya jajirce don ganin cewa kowa ya samu abincin da zai ci ta hanya mai sauki.

 

A cewar Ministan, "Muna yin duk mai yiwuwa don kawo wani taimako wanda zai haifar da raguwar farashin abinci.

 

“A zahiri, ba wanda zai zauna yana zuba ido. Muna yin abin da za mu iya don ganin an inganta harkar noma da kuma samar da abincin da zata ciyar da dimbin al’ummar Najeriya, haka kuma da dabbobi.”

 

A cewar sa, Buhari ya ba da umarnin a kula da cibiyoyin bincike a kasar nan da kyau, kuma shi ne a gaban sa don ganin an inganta aikin bincike domin a inganta amfanin gona.

 

Ya ce gwamnati za ta dawo da tsarin bunkasa ci gaba na GES shekaru kadan bayan soke shi.

 

Ya nuna damuwan sa akan yadda kayayyaki na tallafin noman baya isa kananan manoma.

 

A cewar sa, “Za mu yi duk abin da ya kamata don tabbatar da cewa tsarin da za a fitar ya samu abubuwan da za su taimaka wa kananan manoma daga tushe."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci