OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Muatane 100 Sun Mutu Sakamokon Barkewar Cutar Sankarau a Jigawa

Muatane 100 Sun Mutu Sakamokon Barkewar Cutar Sankarau a Jig

Akalla mutane 100 ne suka mutu sakamakon Barkewar cutar sankarau mai suna Cerebrum Spinal Meningitis (CSM) a jihar Jigawa.

Barkewar cutar da ta fi kamari a kan iyakokin Najeriya da jamhuriyar Nijar, ta yi sanadiyar mutuwar yara ‘yan kasa da shekaru 11.

AllNews ta tattaro rahoton cewa yawancin mutanen da abin ya shafa sun kasance basa samun goyon bayan gwamnati don shawo kan barkewar.

Haka kuma wadanda abin ya shafa sun koka kan rashin samun magungunan da suka dace.

Hakimin kauyen Dungundun, daya daga cikin al’ummar da lamarin ya shafa Malam Alkasim Yakubu ya ce yara 19 ne suka mutu sakamakon barkewar cutar a yankinsa.

Ya ce, “Matsalar ta faro ne tun a watan Afrilu, amma cutar ta ci gaba a watan da ya gabata.

"Al'amarin ya kara ta'azzara wasu makonni baya kuma kamuwa da cuta da mutuwa sun yi yawa," kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Wani hakimin kauye, Bulama na Mele a karamar hukumar Gumel ya bayyana cewa al’ummarsa sun rasa ‘ya’ya 21.

Yayin da aka tabbatar da mutum 70 sun kamu da cutar a karamar hukumar Babura, an samu asarar rayuka 19 sakamakon barkewar cutar.

Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, babban jami’in kula da cututtuka a ma’aikatar lafiya ta jihar Jigawa, Malam Samaila Mahmud ya ce yayin da aka samu rahoton mutane 280 da suka kamu da cutar, an samu mutuwar mutane 65.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati na aiki tukuru domin shawo kan barkewar cutar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci