OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Mo'Allahyidi da wasu 4 sun ki amincewa da zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a Adamawa

Mo'Allahyidi da wasu 4 sun ki amincewa da zaben fidda gwani

Sanata Abubakar Mo'Allahyidi da wasu 'yan takarar kujerar Sanatan Adamawa ta kudu a karkashin jam'iyyar APC su hudu sun yi watsi da sakamakon zaben fidda gwani na jam'iyyar da aka kammala.

Idan dai za a iya tunawa ‘yan takara biyar sun sha kaye a zaben ne a hannun Adamu Ismaila Numan wanda ya samu mafi yawan kuri’u a zaben da aka gudanar a karshen makon da ya gabata.

‘Yan takarar da aka kayar sun bayyana kokensu a wata takardar koke da suka rubutawa kwamitin daukaka kara kan zaben.

Sun yi zargin cewa zaben ya kasance da sayen kuri’u da kuma ayyukan da ba su dace ba.

Sun kuma yi kira da a soke zaben kuma a gudanar da wani sabon zabe.

Daya daga cikin ‘yan takarar da aka kayar, Barista Silas Sanga ya yi zargin cewa wasu ‘yan daba ne na Adamu Ismaila Numan suka kai musu farmaki inda suka lalata musu motocinsu.

Ya kara da cewa a sakamokon haka ne basa cikin zaben.

A halin da ake ciki, Numan ya musanta ikirarin yana mai bayyana shi a matsayin mara tushe.

Sauran ‘yan takarar da aka kayar sun hada da, Sanata Grace Bent Jackson, Bridget Zidon da Sani Jada.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci