Mataimakin kakakin majalisar dattawa Barau I. Jibrin ya jajantawa al'ummar Kano bisa rashin mutum 14 da wata tirela ta murkushe su har lahira bayan sallar Juma’a a jihar Kano.
Sanata Jibrin ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa kan lamarin. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ismail Mudashir ya fitar a ranar Asabar din nan.
A cewar Mudashir, Sanatan ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu ya kuma basu lafiya cikin gaggawa.
Sanarwar a wani bangare na cewa “muna alhinin wannan rashin mutum 14 da wata tirela ta murkushe bayan sallar Juma’a a Kano. Muna mika ta'aziyyarmu"
"Muna addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu ya zaba musu Aljanatul Firdausi, kuma Allah Madaukakin Sarki ya ba wa wadanda suka bari a baya da hakurin jure rashin su."
Allnews.ng ta rawaito cewa, hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta kasa FRSC ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce lamarin ya faru ne a garin Imawa da ke karamar hukumar Kura ta jihar da ke kan hanyar Zariya zuwa Kano.
0 Tsokaci