OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 11 Watanni da suka shude

Majalisar Gombe Ta Amince Da Kasafin Kudi Naira Biliyan 154 Na 2022

Majalisar Gombe Ta Amince Da Kasafin Kudi Naira Biliyan 154

Majalisar dokokin jihar Gombe ta amince da kasafin kudin shekarar 2022 na N154bn wanda gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya gabatar.

An zartar da kasafin N154,963,964,000 ne a ranar Talata yayin zaman majalisar.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban harkokin yada labarai na Majalisar, Abubakar Umar.

Umar ya ce kasafin N154, 610, 614, 000 kamar yadda gwamnan ya gabatar a yanzu ya samu karin N353, 350, 000.

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Gombe, Abubakar Luggerewo ya yaba wa kwamitin kasafin kudi bisa gagarumin aiki da suka yi wajen ganin an zartar da kasafin kudin duk da rashin isashshen lokaci.

Yayin da yake yaba wa gwamnan bisa nasarar da aka samu wajen aiwatar da kasafin kudin shekarar 2021, ya bayyana kasafin na 2022 a matsayin “kasafin jama’a”.

Luggerewo ya kuma yi kira ga sauran kwamitoci da su bada ingantacciyar hidima da hadin kai domin samun nasarar aiwatar da kasafin kudin ba tare da wata matsala ba.

Ya ce, "Ina so in yi kira ga kwamitocin majalisar nan da su himmatu wajen sa ido kan ma'aikatu a karkashin su don samun kyakkyawan aiyuka a wurin aiwatar da kasafin kudin 2022."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai