OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kungiyar Malaman Jami’ar Gombe Ta Jaddada Kudirinta Na Ci Gaba Da Yajin Aikin

Kungiyar Malaman Jami’ar Gombe Ta Jaddada Kudirinta Na Ci

Biyo bayan matakin da Hukumar Gudanarwar Jami’ar Jihar Gombe ta dauka na sake dawo da dalibai 'yan matakin aji daya domin gudanar da karatunsu, reshen kungiyar na Jami’ar ta ce Majalisar Dattawan Cibiyar ce kadai ke da hurumin sasu hakan.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar, Dokta Suleiman Jauro da Sakatare Mohammed Ndogu suka fitar, reshen na goyon bayan yajin aikin ASUU, inda suka kara da cewa har yanzu yajin aikin nanan daram.

Wakilin Jaridar Punch ya ruwaito cewa ASUU sun shiga yajin aiki tun ranar Litinin 14 ga watan Fabrairun 2022 saboda gazawar gwamnatin tarayya na cimma yarjejeniyar da ta kulla.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “An jawo hankalin kungiyar ne kan wata takardar da aka ce mahukuntan jami’ar ta yi na neman dalibai matakin aji daya da su koma karatu da kuma wasu jaridu da ake yadawa cewa an dawo da ayyukan ilimi a Jami’ar Jihar Gombe, Wannan bayanin da ke cikin jaridu ba daidai ba ne.

“Muna fatan ganin cewa bisa ga dokar Jami’ar Jihar Gombe, Majalisar Dattawa na jami'ar ce kadai ke da hurumin amincewa da kalanda don farawa da kuma kawo karshen ayyukan jami’ar, kuma hakan bai faru a jami’ar ba.  yau.”

Yayin da yake kira ga daliban da su zauna cikin shiri, reshen ya bayyana cewa, domin samar da ingantaccen tsarin jami’o’i, mambobinsa za su ci gaba da dagewa har zuwa kyakkyawan karshe, inda ya kara da cewa mambobin ba za su shiga cikin shirin dawowar daliban ba.

 “Bugu da ƙari, ina so in sanar da jama’a sarai cewa malaman Jami’ar Jihar Gombe suna bin umarnin Majalisar Zartarwa ta Ƙasa ASUU na yajin aikin gama gari da ma’ana don samar da ingantaccen tsarin jami’o’i.


“Malamai a karkashin kungiyar ASUU reshen Jami’ar Jihar Gombe ba za su koma aiki ba har sai an janye yajin aikin da ake yi na kasa a halin yanzu, da yardar Allah.  

"Dalibai da Iyaye/Masu kulawa na iya son yin amfani da wannan bayanin cikin hikima don adana lokacinsu, kuzarinsu da ƙarancin albarkatun su,” inji sanarwar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci