OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Wata da ya shude

Kungiyar Likitoci Ta Koka Da Rashin Tsaro A Kogi, Likitoci Na Tserewa

Kungiyar Likitoci Ta Koka Da Rashin Tsaro A Kogi, Likitoci N

Photo Source: Daily Post

Kungiyar likitocin Najeriya (NMA) reshen jihar Kogi ta koka kan matsalar tsaro a jihar, inda ta kara da cewa mambobin kungiyar suna tserewa don gudun a sace su.

Shugaban kungiyar, Dr Abubakar Hassan ne ya bayyana hakan a Lokoja babban birnin jihar.

Da yake bayyana wa bayan wani taron gaggawa, ya ce masu garkuwa da mutane sun kara karfi kuma suna yin aiki ba tare da tsoro ba saboda kokarin jami'an tsaro ya gaza.

Ku tuna cewa an yi garkuwa da wata ma’aikaciyar Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIS), Dakta Rukayat Musa a ranar 21 ga watan Yuni, 2022.

A halin da ake ciki, Hassan ta bayyana cewa wadanda suka sace ta sun sako ta kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kungiyar ta kuma yi kira da gwamnatin jihar Kogi da ta tallafa wajen inganta karfin hukumomin tsaro.

Ya kara da cewa hakan zai taimaka wa jami’an tsaro fuskantar barazanar da karfin gaske. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai