OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Watanni da suka shude

Kudin Abacha: SERAP Ta Kai Karar Buhari

Kudin Abacha: SERAP Ta Kai Karar Buhari

Kungiyar SERAP ta kai karar shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan rashin buga cikakkun bayanai kan yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta kulla da kasar Amurka  na maido da dala miliyan 23 da Marigayi Janar Sani Abacha ya karkatar.

 

A watan Agusta ne gwamnatin Amurka ta kulla yarjejeniya da gwamnatin tarayya na maido wa Najeriya dala miliyan 23 da Abacha ya sace. 

 

A cikin karar da aka shigar a ranar Juma’ar da ta gabata a babbar kotun tarayya da ke Abuja, SERAP na neman kotun ta tilastawa shugaba Buhari da Abubakar Malami su saki kwafin yarjejeniyar da suka kulla da kasar Amurka a fili.

 

 SERAP tana kuma rokon kotun da ta “umartar da kuma tilastawa Shugaba Buhari da Abubakar Malami da su wallafa bayanan tsare-tsaren da aka yi don tabbatar da cewa ba a karkatar da kudaden da aka dawo da su ba, ko kuma a sake sace su a karo na biyu.

 

 Karar da Lauyoyin SERAP Kolawole Oluwadare da Ms Atinuke Adejuyigbe suka shigar a madadin SERAP sun karanta a wani bangare cewa tsarin mulkin Najeriya da dokar ‘yancin bayanai ta bawa kowane dan kasa damar ya bukaci bayanai daga gwamnati.

 

 Rubuce a cikin Karar “Gwamnatin Tarayya tana da alhakin tabbatar da gaskiya da rikon amana a kan yadda ake kashe duk wani kudaden da aka sace da aka dawo da su, domin rage illar cin hanci da rashawa.”

 

Kawo yanzu de ba'a kayyade ranar da za a saurari karar ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai