OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Ku Zaɓi Wata Hanya Ba Yajin Aiki - Rokon Tambuwal Ga ASUU

Ku Zaɓi Wata Hanya Ba Yajin Aiki - Rokon Tambuwal Ga ASUU

Aminu Waziri Tambuwal| Hoto Daga: Vanguard

 
Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya roki kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da ta sauya daga yin yajin aiki a matsayin hanyar shigar da korafin su ga gwamnati. 

Tambuwal ya yi wannan rokon ne yayin da ya karbi bakoncin sabbin shuwagabannin kungiyar na reshen jami’ar jihar Sakkwato a ranar Alhamis.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Muhammad Bello, gwamnan ya bukaci kungiyar kwadagon da ta binciko wasu hanyoyi na "tattaunawar da aka tsara don isa ga yarjejeniya da fahimtar juna tsakanin ta da gwamnati a matakai daban daban amma banda yajin aiki. "

Ya kara da cewa yajin aikin yana shafar ayyukan jami'a, jihohi da ma kasa baki daya.
 
Gwamnan ya kuma yaba wa tsofaffin shuwagabannin da suka gabata saboda kyakkyawan jagoranci da suka nuna. Ya kuma yi kira ga wadanda za su gaje su da "su rungumi tattaunawa ta lumana, sadaukarwa da sasantawa tsakanin kungiyar kwadago, da shuwagabannin jami'oi da masu jagorantar jihar a duk batun da ka iya tasowa a gaba."

Yayin da yake rokon, ya ce, "ba batun rikici bane. Ba batun fada bane. Dukanmu muna da manufofi iri ɗaya, wanda shine inganta darajar ilimi a kowane mataki a jihar. ”

Tambuwal ya yi kira ga gwamnati da ASUU da su hada kai da nufin bunkasa bangaren ilimi.

"A cikin kalaman nasu, tsohon shugaban da sabon shugaban kungiyar reshen jami'ar jihar Sakkwato na ASUU, Dakta Attahiru Sifawa da Dakta Saidu Isah Abubakar sun ce sun je gidan ne domin nuna godiyarsu ga Gwamnan.

"Sun yaba masa saboda fadada jami'ar ta hanyar gina fannoni da dama, gina dakin karatu na jami'a, hadaddun ofisoshi 60, sauran kayan aiki da kuma sabon asibitin koyarwa na jami'ar jihar Sokoto.

"Mutanen biyu sun kuma yi godiya ga gwamnan kan yadda ya sauke dukkan hakkokin ma'aikata yayin da suka roke shi da ya magance matsalar gidajen ma'aikata da aka watsar a jami'ar," in ji sanarwar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci