OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Ku Tabbatar Kuna Da Katin Zabe Don Zabar Shugabanni Na Gari— Khaifa Muhammadu Sunusi II

Ku Tabbatar Kuna Da Katin Zabe Don Zabar Shugabanni Na Gari�

Khalifa Sunusi Lamido Sunusi

Shugaban Jam’iyyatu Ansariddeen (Attijaniyya) na Kasa, Khalifa Muhammad Sanusi ll, ya ‘yan Najeriya nan da su  tabbatar an yi musu katin zabe domin bas u damar zabar ’yan takarar da suka cancanta a zabuka da za’a yi a kasar nan.

Khalifa Sunusi ya yi wannan kira ne ranar Asabar a Lokoja, a yayin rufe taron shekara-shekara karo na Darikar ta gudanar karo na 4 a kasar nan.

A yayin taron mai taken: Hanyoyin samun waraka da suka samo asali daga Annabawa, Khalifan ya bukaci ‘yan darikar su zabi shugabannin da suka cancanci jagorantar al’umma ba tare da la’akari da addinin su ba.

Ya kuma jaddada bukatar ci gaba da yin addu’ar samun zaman lafiya da kuma nisantar tsatsauran ra’ayi, inda ya bayyana fatan daukin ALLAH SWT wajen kawo karshen matsalolin da suka addabi kasar.

Khalifa Sunusi ya kuma yabawa Gwamna Yahaya Bello bisa karbar bakuncin su, da kuma amincewa da ya yi bukatarsu na samar da fili a jihar domin gina cibiyar Musulunci ta kasa da kasa domin karrama Sheikh Muhammad Ibrahim Niass.

Da yake jawabi, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce taron ya zamo ranar tarihi a gare shi da al’ummar jihar baki daya.

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci