Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta samu sammacin kama Diezani Alison Madueke kan zargin almundahana.
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ce ta bayar da sammacin a ranar Litinin.
Sammacin wanda mai shari’a Bolaji Olajuwon ya bayar ya biyo bayan bukatar lauyan EFCC, Farouk Abdullah ya shigar.
Abdullahi ya ce takardar za ta bada daman duk jami’an tsaro da suka hada da INTERPOL su gabatar da Diezani a gaban kotu.
Wannan dai ba shi ne karon farko da aka bayar da sammacin kama Diezani da ta gudu daga kasar zuwa Birtaniya ba tun shekarar 2015.
Diezani Alison Madueke ta kasance ministar albarkatun man fetur a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Gudluck Ebele Jonathan.
A shekarun baya ne hukumar ta EFCC ta kwace wasu kadarori daga hannun Diezani wacce ake tuhuma da karkatar da dukiyoyin jama'a.
0 Tsokaci