OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kotu Ta Bada Umarnin Garkame Wani 'Nurse' Akan Mutuwar Mara lafiya

Kotu Ta Bada Umarnin Garkame Wani 'Nurse' Akan Mutuwar Mara

Wata kotun majistare da ke zamanta a Ibadan ta bayar da umarnin tsare wani ma’aikacin jinya mai shekaru 59, Adesoye Aniwura bisa laifin yin sanadin mutuwar maralafiya a asibitin sa.

Alkalin kotun, Mista Emmanuel Idowu ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin.

Idowu ya ki amincewa da bukatar wanda ake zargin na neman a sake shi.

Alkalin kotun ya kuma umurci ‘yan sanda da su mayar da fayil din karar zuwa ga daraktan kararrakin jama’a (DPP).

Yayin da ake jiran shawarar lauyoyi daga DPP, an dage sauraron karar zuwa ranar 18 ga watan Agusta, 2022.

Wanda ake zargin ya samu wakilcin lauyan sa W. Owoniyi yayin da lauyan wanda ya shigar da karar ya kasance E.O. Ayola.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa, “dan sanda mai shigar da kara, Insp Iyabo Oladoyin, ta shaida wa kotu cewa Aniwura, a ranar 28 ga watan Mayu, da misalin karfe 3 na safe a asibitin sa, ya yi sanadin mutuwar wata Esther Oladepo mai shekaru 24, ta hanyar tiyatar da aka yi mata har sau uku wanda ya kai ga mutuwar ta."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci