OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Watanni da suka shude

Jam'iyyar APC Ta Dage Ranar Kaddamar Da Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Ƙasa

Jam'iyyar APC Ta Dage Ranar Kaddamar Da Fara Yakin Neman Zab

Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ta dage ranar fara yakin neman zaben wanda aka shirya zai gudana a ranar Laraba.

Darakta-Janar na kungiyar yakin neman zaben, Gwamna Simon Lalong na jihar Filato shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

“A baya mun shirya yin tattaki da addu’o’i a ranar Laraba, don fara yakin neman zaben shugaban kasa na shekarar 2023 a hukumance.

“Mun kuma sanar da cewa mambobin kwamitin yakin neman zaben su bayyana a hedkwatar yakin neman zaben a ranar domin karbar takardar tabbatar da nadin su.

"Amma Saboda karin jerin sunayen masu ruwa da tsaki da bukatun cikin gida na jam'iyyar, mun yanke shawarar chanza ranar fara wadannan ayyukan," in ji shi.

Ya bayyana cewa, an yi hakan ne domin tabbatar da cewa kowa ya sami halartar ayyukan da za a yi a hukumance.

 Ya kara da cewa sanarwar da aka bayyana cewar za a fara gangami yakin neman zabe 28 ga watan satumba an dage sai zuwa gaba za a sake bayyana rana.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai