OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Jami’an Tsaro Sun Yi Ram Da Kansila Dauke Da Ak-47 Kusa Da ‘yan bindiga a Kaduna

Jami’an Tsaro Sun Yi Ram Da Kansila Dauke Da Ak-47 Kusa Da

Jami’an tsaro sun kama wani kansilan karamar hukumar Soba dauke da bindiga kirar Ak-47 a kusa da yankin ‘yan bindiga a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

An bayyana kansilan da suna Abdul Adamu Kinkiba.

A cewar majiyoyi, an kama Kinkiba ne a kan babur kusa da yankin ’yan bindigar da ke addabar al’umma.

Majiyoyi sun bayyana cewa kansilan ya ce ya karbi bindigar ne daga hannun wani da bai san sunan sa ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wata majiya ta ‘yan banga ta bayyana cewa kansilan ya ce “An gaya masa cewa bindigar ta ayarin motocin wani ne.

“A cewarsa, an umarce shi da ya yi fakin bayan gadar da ke kusa da dajin Galadimawa (wani maboyar ‘yan bindiga), inda wani zai karbe bindigar.”

A halin da ake ciki shugaban karamar hukumar Soba wanda ya kadu da faruwar lamarin ya tabbatar da wanda ake zargin a matsayin kansila daga unguwar Kinkiba a karamar hukumar.

Ya kuma ki yin karin bayani kan lamarin inda ya danganta shirun da ya yi da kaduwa da samun labarin.

A halin yanzu dai tuni aka mika wanda ake zargin zuwa hedikwatar rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke jihar Kaduna.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai