OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

ISWAP ta dau Alhakin kai harin gidan gyaran hali na Kuje

ISWAP ta dau Alhakin kai harin gidan gyaran hali na Kuje

A ranar Larabar ne kungiyar IS da ke yammacin Afirka (ISWAP) ta ce mambobinta ne suka kai hari a gidan gyaran hali na Kuje da ke Birnin Tarayya, Abuja.

Ku tuna cewa an kai harin ne a ranar Talata inda aka sako fursunoni sama da 600.

An samu rahotannin cewa ba a gano tsohon shugaban rundunar ‘yan sanda na musamman da aka tsare a gidan ba wato Abba Kyari.

Sai dai cibiyar ta musanta rahoton.

Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar ISWAP ta fitar da faifan bidiyo na mambobinta da ke aiwatar da wannan aika aikan. 

Idan dai za a iya tunawa, AllNews ta ruwaito cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuma ziyarci wurin domin tantance irin barnar da aka yi a wurin. 

Shugaban yayin ziyarar tasa a ranar Laraba inda ya nuna rashin jin dadin sa kan harin yana mai zargin jami’an tsaro masu daukan sirri da yin kasa da yadda aka zata.

Ya Kara da cewa lallai sun bashi kunya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci