OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Inuwa Yahaya Zai Gabatar da Kasafin Kudi na 2022 A Yau

Inuwa Yahaya Zai Gabatar da Kasafin Kudi na 2022 A Yau

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya| Hoto Daga: ThisNigeria

A yau ne gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2022 ga majalisar dokokin jihar.

Ana sa ran gabatar da kasafin kudin zai fara da karfe 11 na safe.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban daraktan sa kan harkokin yada labarai Ismaila Uba Misili.

Hakan ya zo ne biyo bayan amincewa da kudirin kasafin kudin yayin zaman majalisar zartarwar jihar a ranar Litinin.

Kwanakin bayan nan ne gwamnan ya tattauna kan kasafin a wani taro da ya yi da sarakunan gargajiya da shugabannin al’ummomi da kungiyoyin kwadago da kuma kungiyoyi masu zaman kansu domin basu damar sa baki cikin aiwatar da mulkin.

Za a watsa gabatar da kasafin kudin ne kai tsaye daga harabar majalisar dokokin jihar ta gidajen rediyon jihar da kuma kafafen sada zumunta.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci