OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 3 Watanni da suka shude

Inuwa Yahaya Ya Ziyarci Kwalejin Shari'a a Nafada, Yayi Alkawarin Gyara

Inuwa Yahaya Ya Ziyarci Kwalejin Shari'a a Nafada, Yayi Alka

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya jaddada kudirin sa na inganta ilimi a lokacin da ya ziyarci kwalejin ilimi da nazarin shari’a ta Nafada.

Gwamnan ya sha alwashin kammala ginin dakunan kwana na mata da aka yi watsi da su da sauran ayyuka a makarantar.

A shekarar 2018 ne aka yi watsi da ginin dakunan kwanan dalibai mata da aka fara ginawa.

Yahaya ya ce duk da rashin kudi gwamnatin sa na ci gaba da jajircewa wajen farfado da harkar ilimi a jihar.

A cewar wata sanarwa da babban daraktan yada labarai na gwamnan, Ismaila Uba Misilli ya fitar a ranar Laraba, gwamnan da ya ziyarci makarantar domin tantance kalubalen gine-gine a makarantar ya ce gwamnatin sa na shirin samar da wurin zama na dindindin don sake gina makarantar.

A cewar gwamnan: "Ziyarar duba kayayyakin da muka fara za ta taimaka mana a matsayinmu na gwamnati wajen tantance abubuwan da ke faruwa a kasa da kuma rubabben da ke cikin Makarantun mu da nufin daukar matakan da suka dace tare da samar da wuri na dindindin".

Yahaya ya kara da cewa, "Muhalin ilimi ko kuma wata kafa ta Gwamnati na bukatar wurin dindindin domin samun damar kafa gine-ginen da za su iya tsayawa tsayin daka ba kamar tsarin da ba shi da inganci a yanzu," in ji Yahaya.

Haka kuma kwamishinan ilimi mai zurfi, Mista Meshack Audu Lauco ya ce ziyarar Gwamnan za ta share fagen kawo sabbin gine-gine a makarantar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai