OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Inuwa Yahaya ya ziyarci Iyalan marigayi Dattijo Hassan Santana don ta'aziyya

Inuwa Yahaya ya ziyarci Iyalan marigayi Dattijo Hassan Santa

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya ziyarci iyalan marigayi dattijon jihar, Hassan Muhammad Santana domin ta'aziyyar rasuwar sa.

Gwamnan ya kai ziyarar ta’aziyyar ne a yau a gidan marigayi Santana da ke Jekadafari.

Marigayi Santana ya rasu ne bayan ya sha fama da jinya ranar Asabar a Gombe yana da shekaru 80 a duniya.

A cewar mai magana da yawun gwamnan, Ismaila Uba Misilli a cikin wata sanarwa, gwamnan yace: “Bayan na halarci sallar jana’izar marigayin, har yanzu ina ganin ya dace in jagoranci tawagar gwamnatin jihar Gombe da kai na domin ta’aziyyar wannan iyali masu mutunci. 

"A madadin iyalai na da gwamnati da kuma al'ummar jihar Gombe, ina mika sakon ta'aziyyar mu a gare ku bisa wannan babban rashi da aka yi da kuma addu'ar Allah Ta'ala ya bamu ikon juriyar rashin, ya kuma zurta mamacin da Aljannar Firdausi".

Gwamnan ya kuma bayyana rasuwar sa (Santana) a matsayin rashin wani babban ginshiki a jihar.

Ya kara da cewa marigayi dattijon ya bayar da gudunmawa da dama ga al’umma.

Gwamnan a cikin wata sanarwa da ya fitar a baya ya bayyana marigayi Santana a matsayin "Uban kishin kasa da misali, dan siyasa mai kishin kasa kuma babban jagoran al'umma wanda ya yi tasiri ga rayuwar mutane da dama."

Gwamnan ya kai ziyarar tare da wasu fitattun jigajigan gwamnati da suka hada da shugaban ma’aikatan fadar sa Abubakar Inuwa Kari.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci