OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Inuwa Yahaya Ya Yi Jimamin Rasuwar Sarkin Funakaye Mai Shekaru 45

Inuwa Yahaya Ya Yi Jimamin Rasuwar  Sarkin Funakaye Mai Shek

Late Emir of Funakaye, Alhaji Mu'azu Muhammad Kwairanga

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana jimamin sa game da rasuwar Sarkin Funakaye, Alhaji Mu'azu Muhammad Kwairanga.

Gwamnan wanda ya samu labarin rasuwar ya bayyana hakan a matsayin babban rashi ga masarautar Funakaye da ma jihar da Najeriya baki daya.

A cewar babban daraktan yada labarai na gwamnan, Ismaila Uba Misilli a wata sanarwa da ya fitar, Yahaya ya bayyana cewa: “Hakika jihar Gombe ta yi rashin daya daga cikin manyan sarakunan gargajiya da suka yi aiki tukuru tare da sauran sarakunan jihar tare da ba da shawarwari da jagoranci ga zaman lafiya, hadin kai, ci gaban jihar musamman da Najeriya baki daya."

Yahaya ya ci gaba da bayyana marigayi Sarkin a matsayin mai tawali’u, mai mutunci da sauke kai wanda ya kula da talakawan sa, da kuma hadin kai da ci gaban jihar, inda ya bayyana watanni 16 da ya yi yana mulki a matsayin abin azo a gani ne. 

“Don haka Gwamnan ya mika sakon ta’aziyyar sa a madadin gwamnati da al’ummar jihar Gombe, ga iyalan gidan sarautan, da al’ummar Masarautar Funakaye, da Shugaban Majalisar Sarakuna da Sarakunan Jihar Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar lll da kuma gabadaya Jihar Gombe kan wannan babban rashi da aka yi, muna addu’ar Allah Madaukakin Sarki da ya sanya marigayin a Aljannar Firdaus," kamar yadda sanarwar ta bayyana. 

Marigayi Sarkin ya rasu ne a jiya, 27 ga watan Agusta, 2022 yana da shekaru 45.

Za'ayi Sallar Jana'izar ne a yau (Lahadi) 28 ga Agusta, 2022 da karfe 2:00 na rana a fadar mai martaba Sarkin Bajoga, karamar hukumar Funakaye ta jihar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai