OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Watanni da suka shude

Inuwa Yahaya Ya Kafa Kwamitin Riko Na Cibiyar Masana'antu

Inuwa Yahaya Ya Kafa Kwamitin Riko Na Cibiyar Masana'antu

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya kafa kwamitin riko na gudanar da aikin cibiyar masana'antu na jihar.

Cibiyar masana'antun da aka sanya wa sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari yana Dadinkowa a karamar hukumar Yamaltu Deba.

Sakataren gwamnatin jihar Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ne ya bayyana hakan a ranar Talata.

A cewar sa, kwamitin zai dauki nauyin samar da tsarin da ya dace don Gudanarwa da fara aikin wurin.

Ya kara da cewa an dauki wannan matakin ne domin samar da yanayi mai kyau na jawo hankalin masu zuba jari na cikin gida da waje a jihar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Ismaila Uba Misilli ya sanya wa hannu: “Kwamitin a cewar sakataren, yana da Bashir Mohammed Aliko a matsayin shugaba tare da Mista Adamu Wuri Lubo, Engr. Bala Adams da Aishatu Abdulkadir Rasheed yayin da Mu’awiya Farouk, Manajan Daraktan Kamfanin Zuba Jari da Rarraba Kadarori na Jihar Gombe (GSI&PDC) zai zama Sakatare.

"Dukkan nadin zai fara aiki nan take."

A halin da ake ciki gwamnatin jihar na ci gaba da aikin gine-gine a filin masana'antar na Muhammadu Buhari.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai