OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Inuwa Yahaya Ya Hada Kai Da Kamfanin MTN Domin Inganta Kiwon Lafiya

Inuwa Yahaya Ya Hada Kai Da Kamfanin MTN Domin Inganta Kiwon

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya hada kai da kamfanin sadarwa na MTN domin inganta harkokin kiwon lafiya.

Haɗin gwiwar ya zo ne tare da ƙaddamar da asibitin kula da lafiyar tafi-da-gidanka don biyan bukatun ayyukan kiwon lafiya.

A wajen bukin kaddamarwar, Yahaya ya ce hadin gwiwar zai karfafa bangaren lafiya wanda yake fuskantar kalubale sakamakon yawan bukatar mutane.

Ya kara da cewa gwamnatin sa a bude take ga duk wani tunanin da zai kawo karshen wahalhalu ga al’ummar jihar.

Yayin da yake tabbatar da goyon bayan gwamnatin sa, gwamnan ya yaba da kokarin MTN na inganta rayuwa a jihar ta hanyar hadin gwiwa.

Da yake jawabi a wajen taron, kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Habu Dahiru ya bayyana cewa asibitin tafi da gidanka zai yi amfani ga mazauna karkara wajen samar da ingantacen kiwon lafiya.

Ya kara da cewa asibitin tafi-da-gidankan na kunshe da shawarwari kyauta don ciwon sukari, zazzabin cizon sauro, hepatitis B da HIV.

Ya bayyana cewa, "Za a ba da magunguna kyauta ga majinyata da suka cancanta yayin da za a ba da shawarwari ga waɗanda za su buƙaci ƙarin kulawa."

Babban jami’in hulda da jama’a na kamfanin sadarwa na MTN a jihar Gombe, Harrison Thliza ya bayyana cewa hadin gwiwar da aka yi da su don magance wasu manyan matsalolin da jihar ke fuskanta ne.

Yayin da yake bayyana cewa asibitin tafi da gidankan zai ba da allurar COVID-19, haka kuma, "Wannan asibitin za ta mayar da hankali kan bincike da bada maganin gudawa, zazzabin cizon sauro, cututtukan numfashi, gwajin ciwon sukari, HIV, hepatitis da sauran su."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci