OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Hukumar NYSC Ta Ce Sai Da Rigakafin Korona Zata Bar Masu Hidimtawa Kasa Su Shiga Sansani

Hukumar NYSC Ta Ce Sai Da Rigakafin Korona Zata Bar Masu Hid

Hukumar kula da masu yiwa kasa hidima, NYSC ta ce daga yanzu babu dan hidimar kasa da zai shiga sansani ba tare da rigakafin korona ba.

Shugaban hukumar, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim ne ya bayyana hakan cikin watan sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Ya ce hukumar ta dauki matakin ne domin kare lafiya da rayukan masu hidimtawa kasar.

Da yake yi wa jami'an hukumar da suka kula da Rukunin C  jawabi, Janar Ibrahim ya ce daga yanzu sai masu yi wa ƙasa hidimarsun nuna katin shaidar rigakafin kafin su shiga sansani.

Shugaban ya kuma ja kunnen masu yiwa kasa hidima da su guji tafiya cikin dare saboda matsalar tsaro da ake fama da shi a fadin kasar nan.

Haka ya kuma shawarce su da su mayar da hankali wajen amfani da abubuwan da suka koya a sansanin domin tsayawa da kafafun su bayan sun kammala hidimtawa kasar.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci