OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Hukumar NSCDC Ta Yi Ram Da Gungun Masu Satar Shanu A Jihar Zamfara

Hukumar NSCDC Ta Yi Ram Da Gungun Masu Satar Shanu A Jihar Z

Nigeria Security and Civil Defense Corps (NSCDC)

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) ta kama wasu barayin shanu biyu a Zamfara.

An kama wadanda ake zargin ne a ranar Litinin a tashar mass na jihar Zamfara da ke Gusau.

Kakakin hukumar NSCDC na jihar Zamfara, Mista Oche Ikor ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa wadanda ake zargin sun hada da Hussaini da Abubakar Altine.

An kama wadanda ake zargin ne a lokacin da suke tafiya jihar Taraba domin haduwa da ‘yan uwan su da suka tafi kafin su.

Daya daga cikin wadanda ake zargin ya amsa laifin satar shanu da dama wanda ya yi sanadin kashe akalla mutane shida.

Ya ce, “Muna hayar bindigu ne don mu kashe mutane, kuma zan iya shaida muku cewa na taka rawa wajen kai hare-hare da dama a kan al’ummomi daban-daban a lokuta daban-daban, ana biyan mu Naira dubu goma bayan kowane aiki."

Ya kuma yi ikirarin cewa ‘yan fashin suna haduwa ne a karamar hukumar Birnin Magaji kafin su je aikinsu na haram.

Ya kuma musanta sanin inda shugabannin su ke samun bindigu domin gudanar da ayyukan.

Bayan kama su, ana gudanar da cikakken bincike kuma za a fitar da sakamakon, in ji mai magana da yawun hukumar NSCDC.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai